Jam’iyyar Labour Ta Kori Doyin Okupe Daga Jam’iyyar

Jam’iyyar Labour a Jihar Ogun ta kori, Doyin Okupe a matsayin Darakta Janar na amfen din dan takarar Shugaban Kasa, Peter Obi.

An kori Okupe ne tare da wasu mutum 10 bisa zarginsa da laifin rashin biyan kuɗin shiga ga jam’iyya.

Shugaban jam’iyyar a jihar Ogun, Michael Ashade, ya sanar da matakin da jam’iyyar ta dauka a Abeokuta a yau Alhamis, inda ya ce laifukan sun sabawa kundin tsarin mulkin jam’iyyar Labour.

Ashade ya ce Okupe yanzu ba memba na LP bane saboda “rashin cika ka’idojin tsarin mulki na wajibi don cika matsayin sa na zama cikakken ɗan jam’iyya.”

A cewarsa, Okupe ya gaza biyan hakkokinsa na zama mamba tun watanni shida da komowar sa jam’iyyar, inda ya ce ya yi watsi da matsayinsa na jam’iyyar Labour, don haka bai cancanci zama Darakta-Janar na kwamitin yakin neman zaben Obi ba.

Ya bayyana cewa laifukan Okupe, da sauran mutane goman sun saɓa wa sashe na 9(3) sub(iii) da sashe na 9(3)xi na kundin tsarin LP.

Ya zargi Okupe da karkatar da kudaden da aka amince wa kungiyar ta LP a Ogun domin tara yan jam’iyya a taron gangamin da aka gudanar a makon jiya a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Yayin da suke sanar da shugaban jam’iyyar LP na kasa Barr Julius Abure shawarar da suka yanke, sun yi kira ga Obi da ya gaggauta nada wani DG ga PCC daga Arewa.

Labarai Makamanta