Jam’iyyar APC Ta Yaba Juriyar ‘Yan Najeriya

Rahoton dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyyar APC mai mulki ta sanar da cewa ta yanke hukuncin kafa kwamitin kasafi da sauran kwamitoci gabanin babban taronta na ƙasa a watan Fabrairu.

Da yake jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan taron kwamitin rikon kwarya, sakataren APC na ƙasa, Sanata James Akpanudoedehe yace Jam’iyyar ta yaba da jinjina wa juriya da hakurin ‘yan Najeriya, sannan kwamitinsu ya sake nazari kan ayyukan da ya gudanar tsawon shekara daya.

A baya-bayan nan ne jiga-jigan APC na ƙasa suka gana da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a gidan gwamnatinsa Aso Rock, kan wasu kalubale da Jam’iyyar ke fuskanta a jihohi.

Yayin wannan ganawa ta su ne, suka amince da cewa za’a gudanar da babban taron APC na ƙasa a watan Fabrairu, amma ba su zaɓi rana ba.

Kazaika a taron kwamitin (CECPC) ƙarƙashin jagorancin gwamna Mala Buni, ya gaza sanar da ainihin ranar da taron zai gudana a watan Fabrairu.

“A taron kwamitin rikon kwarya (CECPC) na APC karo na 18 da ya gudana a sakateriyar jam’iyya ta ƙasa ranar 20 ga watan Disamba ya yi duba zuwa ga ayyukan da ya gudanar tsawon shekara ɗaya.”

“Kwamitin ya kuma tattauna kan batutuwa da dama kuma ya cimma matsaya kamar haka: Game da taro na ƙasa an yanke kafa kwamitin kasafin kudi da sauran kwamitin da suka shafi taron.”

Labarai Makamanta