Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Sansanin Bello Turji

Labarin dake shigo mana daga Jihar Sokoto na bayyana cewar jami’an tsaro sun kaddamar da wani harin haɗin gwiwa sansanin ɗan ta’addan na Bello Turji.

An ruwaito cewa an kama wani likita da ake zargin ya yi jinyar harbin bindiga ga dan ta’adda Bello Turji an kama likitan mai suna Abubakar Kamarawa ne a wani gagarumin samame da jami’an tsaro suka kai kan ‘yan ta’addan.

An kama shi ne tare da wasu ‘yan ta’addan a wasu ayyuka daban-daban a fadin kananan hukumomi uku na jihar Sokoto kamar yadda rahotanni suka nuna.

Kananan hukumomin sun hada da, Illela, Rabah da Goronyo, duk a yankin gabashin jihar Sokoto dake fama da matsanancin kalubalen tsaro.

Dr Abubakar ya amince cewa yana jinyar ‘yan bindigar da suka samu raunuka a wani artabu da jami’an tsaro tare da kawo musu kayan buguwa ya fadi dalla-dalla yadda ya yi wa Turji jinya bayan samun raunin harbin bindiga a kai kimanin shekaru uku da suka wuce.

Jaridar Aminiya ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 31 ga watan Junairu 2022, ta tabbatar da cewa jami’an tsaro sun kai wani farmaki, sun yi ram da yaran Bello Turji.

Dakarun ‘yan sandan na Najeriya sun yi dace sun damke wadannan ‘yan bindiga ne da suka kai farmaki a garuruwan Goronyo, Rabah da Illela duk a Sokoto. Mataimakin sufeta na ‘yan sanda, DIG Zaki M. Ahmad ya jagoranci farmakin da aka kai, har aka kama mutane 37 da ake zargin cewa miyagun ‘yan bindiga ne.

An kuma cafko gama-garin mutane 20 da ake tuhuma da laifin alaka da wadannan ‘yan bindiga.

Labarai Makamanta