Jami’an Tsaro Sun Samu Gagarumar Nasara A Jihar Neja

Labarin dake shigo mana daga Mina Babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar Rundunar tsaron hadin gwiwa a jihar sun kama masu laifi 28 sannan sun samo layuka iri-iri, kamar yadda hukumar ‘yan sanda ta bayyana a ranar Talata.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya ce an gudanar da aikin na hadin gwiwa ne tsakanin jami’an soji, DSS, yan sanda, NSCDC da yan banga.

Ya ce dakarun sun kai wani gagarumin samame tare da binciken gida-gida a Unguwar-Biri da ke karamar hukumar Bosso a ranar 25 ga watan Janairu.

“Aikin zai ci gaba da gudana domin tsamo duk wasu bata-gari har sai an raba birnin da miyagu. Kwamishinan yan sandan jihar Neja, CP Monday Bala Kuryas, fsi ya gargadi duk masu tayar da zaune tsaye da su daina ko su hadu da fushin doka.”

“Dukkan wadanda ake tuhuma suna karkashin bincike a SCID, Minna kuma za a gurfanar da su a gaban kotu domin hukunta su da zarar an kammala bincike.”

Abubuwan da aka kwato daga miyagun sun hada da kibiyoyi 10, adduna guda bakwai, wukake takwas, sanduna tara, bututun shisha biyar, abun yankan itace daya, gatari daya, sandar karfe daya, abun yankan karfe daya, almakashi daya.

Sauran kayayyakin sune sukun-direba guda biyu, wayoyin hannu 13, buhuna 17, ledoji tabar wiwi guda hudu, layoyi iri-iri da wasu tufafi da silifas.

Labarai Makamanta