Jama’atu Nasril Islam Ba Zata Halarci Mukabala Da Abdul-Jabbar Ba

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta ƙasa ƙarƙashin jagorancin Shugabanta mai alfarma Sarkin Musulmi Dr Sa’adu Abubakar, ta bayyana cewar ba zata samu damar halartar mukabala da gwamnatin Kano ta shirya gudanarwa tsakanin Abdul-Jabbar da Malaman Kano ba.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwa da ta samu sanya hannun babban Sakataren Ƙungiyar Dr Khalid Abubakar Aliyu, kuma aka rarraba ta ga manema labarai a Kaduna.

Kungiyar ta Jama’atu ta bayyana kalaman da Abdul-Jabbar ke amfani da su a janibin Manzon Allah SAW da Sahabbai, a matsayin cin mutuncin da taɓa darajar Annabi SAW, bisa ga haka hatsari ne babba a gudanar da zama da mutumin da ke irin wadannan miyagun maganganu.

“Babu mai shakkar katoɓarar da Abdul-Jabbar ke yi ga janibin Manzon Allah, gudanar da zama da shi akan hakan kamar taimaka mishi ne wajen yaɗa kalamanshi munana akan Manzon Allah, bisa ga haka Jama’atu ba zata halarci zaman ba, hakazalika dukkanin rassan Ƙungiyar dake Jihohi”

“Kungiyar ta Jama’atu tun da fari ta yaba matakin da gwamnatin Kano ta ɗauka na daƙile dukkanin wata fitina da ka iya tasowa ta dalilin kalaman AbdulJabbar, amma duk da haka ya kamata gwamnatin ta sake faɗaɗa tunaninta akai, domin kuwa wannan al’amari ne babba ba jihar Kano ko Najeriya kadai ya shafa ba, babban al’amari ne da ya shafi duniya gaba daya ya dace a kiyaye”.

Kungiyar ta Jama’atu ta kuma yi fatan alkhairi ga malaman da zasu halarci zaman muƙabalar da yi musu kyakkyawar fata, amma duk da haka tana ƙara kira ga Gwamnatin jihar Kano da sake nazari da yin duba akan matsayin da ta ɗauka.

Abdul-Jabbar Nasiru Kabara dai na fuskantar suka daga ɓangarorin Malamai a jihar Kano bisa ga yadda yake gudanar da karatuttukan shi, lamarin da Malaman ke gani ya yi hannun riga da yadda tsarin karantarwar take tun asali.

Daga bisani ne Gwamnatin Jihar Kano ta shigo cikin lamarin har ta kai ga kulle Masallachin da Abdul-Jabbar ke gudanar da karatu tare da shirya gudanar da mukabala tsakanin shi da sauran malamai, wanda aka tsara yi a ranar Lahadi mai zuwa 07 ga wannan wata na Maris da muke ciki a birnin Kano.

Labarai Makamanta