Jama’atu Da CAN Sun Yaba Ƙoƙarin Mata Masu Yaƙi Da Covid 19

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam reshen Jihar Kaduna da takwarar ta Ƙungiyar Kiristoci CAN ta Jihar sun yaba gami da Jinjinawa kokarin gamayyar kungiyoyin Mata masu yaƙi da cutar Covid 19 a faɗin Jihar Kaduna.

Babban Sakataren Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam ta Jihar Kaduna Malam Ibrahim Kufena ya yi wannan yabon a madadin Ƙungiyar, lokacin da tawagar matan suka ziyarci ofishin Ƙungiyar dake Kaduna.

Ibrahim Kufena ya bayyana cewar Ƙungiyar ta Jama’atu na da rassa na kananan hukumomi guda 23 a faɗin Jihar, kuma babban abin da suka sanya a gaba shine ilimantarwa gami da wayar da kan jama’a akan yadda za su kare kansu daga kamuwa da cutar.

Bisa ga haka Ƙungiyar ta Jama’atu ta yaba ƙoƙarin kungiyar matan akan namijin ƙoƙarin da suke yi na wayar da kan jama’a, tare da yin alkawarin bayar da dukkanin goyon bayan da ya kamata domin samun nasara.

Shima anashi bangaren Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta ƙasa reshen Jihar Kaduna CAN Joseph Hayab ta bakin Sakataren riko na kungiyar Caleb Maaji, ya tabbatar da bada goyon bayan Ƙungiyar CAN akan ayyukan Matan wanda ya bayyana da cewar aikin Allah ne.

Sakataren na CAN ya kara da cewar yana da tabbaci da kwarin gwiwa akan Allah zai taimake su akan aikin jin kai da suke, kuma suna addu’a a kusan kullum da rokon Ubangiji ya kawo karshen wannan cuta.

Tun farko da take gabatar da jawabi Jagorar Ƙungiyar Matan Dr. Lydia Umar ta bayyana cewar, babban kudirin da kungiyar tasu ta sanya a gaba shine taimakon gwamnatin jihar Kaduna wajen ƙara wayar da kan jama’a dangane da yadda za su kare kansu daga cutar.

Ta kara da cewar gamayyar kungiyoyin suna da Mata akalla 30 wadanda dukkanninsu suna jagorantar kungiyoyi daban daban wadanda aka samar domin wayar da kan jama’a da yaki da wannan cuta ta Covid 19.

Labarai Makamanta