Jama’ar Mahaifar Shugaban Kasa Na Neman A Yi Musu Jiha

Al’ummar mahaifar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari dake Daura Jihar Katsina sun gabatar da neman bukatunsu na ayi musu sabuwar jiha daga Jihar Katsina wanda hakan zai taimaka musu wajen sake inganta rayuwar al’ummar su.

Al’ummar sun bayyana hakan ne a lokacin da suka gabatar da jawabi a gaban Kwamitin da ke sake gyaran fuska a tsarin mulkin Najeriya wanda ya yi zama a Jihar Kaduna.

Da yake ƙarin haske akan kudirin nasu mai girma Salanken Daura Alhaji Salisu Yusuf, yace kananan hukumomi 17 ne a yanzu suka haɗe wajen neman sabuwar Jihar wadda suka bata suna da Jihar Bayajjida.

Salanken Daura ya ƙara da cewar akwai jihohi 11 dake yankin Katsina ta Arewa wato mazaɓar Daura, sai kuma ƙananan hukumomi guda 7 dake masarautar Kazaure jihar Jigawa.

Salisu Salanken Daura yace wannan kudiri nasu na neman jiha ba sabo ba ne domin kuduri ne wanda suka fara shi tun a shekarar 1991 wato kimanin shekaru 30 da suka gabata.

“Mun nemi Jihar Bayajjida a shekarar 1991, sannan muka sake nema a shekarar 1995 sannan a wannan karon ma mun sake fitowa neman, kuma mai girma shugaban kasa na tare damu a tafiyar”.

Labarai Makamanta