Jama’ar Kaduna Za Su Yi Murna Da Salon Mulkin Gwamna Uba Sani – Ahmad Maiyaki

An bayyana sabon zaɓaɓɓen Gwamnan Jíhar Kaduna Sanata Uba Sani a matsayin jajirtacce kuma kwararre a wajen iya mulki wanda jama’ar Jihar Kaduna za su yi murna da farin ciki da salon mulkinsa.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin wani jigo a Jam’iyyar APC ta Jihar Kaduna Alhaji Ahmed Maiyaƙi a sakon taya murna da fatan alheri da ya yi wa gwamnan a zantawarshi da Wakilinmu a Kaduna.

Maiyaƙi ya ƙara da cewar kasancewar Uba Sani a matsayin gwani duba da kwarewar da ya nuna a zaman majalisar dattawa da ya yi, inda ya gabatar da kudurori 32 a majalisa wanda Shugaban Ƙasa ya amince da biyu suka zama doka, wannan kyakkyawar alama ce dake gwada cewa jama’ar Jihar Kaduna ba su yi zaɓen tumun dare ba.

“Ina da tabbacin Uba Sani zai ɗora bisa kyawawan ayyukan da El-Rufa’i ya yi, da yin gyara a inda aka samu kuskure domin ciyar da jihar Kaduna gaba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply