Jajirtaccen Shugaba: Kasar Guinea Bissau Za Ta Karrama Buhari

Gwamnatin Guinea Bissau za ta karrama shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da lambar girmama mafi a kasar.

Za ta karrama shugaba Buharin ne bisa la’akari da gudummuwar da yake bayarwa wajen daidaitawa da bunkasa demokuradiyya a shiyyar Afirka ta yamma.

Shugaban kasar Guinea Bissau, Umaro Sissoko Embalo shi ne zai lika wa shugaba Buharin lambar yabon, a wani gagarumin biki da aka shirya a kasar.

Wata sanarwar da mai taimaka wa shugaban Najeriya a kan harkar yada labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar ta ce gwamnatin Guinea Bissau din ta yanke shawarar karrama shugaba Buharin da lambar yabo ko girmamawa mafi daukaka ne sakamakon gagarumar gudummuwar da yake bayarwa wajen raya dimokuradiyya a shiyyar Afirka ta yamma.

Kuma wannan ne ya sa shugaban kasar, Umaru Sissoko Embalo da kan sa ya gayyaci shugaban Najeriyar zuwa Guinea Bissau domin a yi bikin karramar a fadar gwamnati.

Bayan lambar yabon, a cewar sanarwar, yayin bikin akwai wani titi da za a raɗa masa sunan shugaba Muhammadu Buharin duka a cikin Bissau, babban birnin kasar.

Bikin dai kamar yadda sanarwar ta fayyace zai mai da hankali ne wajen yin bayani a kan rawar da shugaba Buharin ya ke takawa wajen yin jagorancin da ya kasance abin koyi a shiyyar Afirka ta yamma musamman ma kasar Guinea Bissau.

Akwai kuma batun kwaɗaita wa shugabanni kyawawan dabi’u na son zaman lafiya da siyasa irin wadda ake damawa da kowa da kowa da nuna halin gima ko mutunci, tare da karfafa tsare-tsaren tattalin arziki don cigaban al’ummomin shiyya baki daya.

Wata ribar-kafa atttare da bulaguron, kamar yadda Mallam Garba Shehu ya ce da shugaba Buhari da takwaransa na kasar Guinea Bissau za su yi amfani da wannan dama wajen tattaunawa a kan hanyoyin ciyar da kasashen nasu gaba.

Labarai Makamanta