Jahilci Na Damun Shugabannin Najeriya – Bugaje

An bayyana shugabannin Nigeria a matsayin wanda suka rasa gogewa, da ilmi da ake buƙata wajen jagorancin ƙasa, da ceto ta akan matsalolin ta.

Tsohon Ɗan Majalisar Nigeria Usman Bugaje ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a Maitama Sule akan wani taro na lekca akan shugabanci, wanda Gamayyar Ƙungiyoyin Arewa a Minna, Babban birnin Niger suka shirya.

Bugaje yace sake canje-canje da ake ta nema bashi ne maganin matsalolin Nigeria, inda yace shugabanci nagari kaɗai zai iya magance matsalolin dake fuskantar ƙasar, kuma shekaru 20 da akayi ana mulki ya sanya yanzu babu yarda tsakanin Gwamnati da Al’umma.

Yace “shekaru 20 a tsarin Dimokuraɗiyya, yanayin cin hanci da talauci na ƙara ƙarfi. Mun tambayi kanmu, miyasa Dimokuraɗiyya bata aiki, miyasa ba’a yi mana aikin da muke buƙata? Ana buƙatar ayi wani abu da gaggawa, bawai maganar wani canje-canje, amma canje-canjen sai da a ɓangaren shugabanci.

Tsohon Ɗan takarar Gwamnan Katsina, ya buƙaci matasa da kada su kaɗa kuri’a, da bada goyon baya ga wani ɗan siyasa a makance a zaɓe mai zuwa, inda ya jaddada bukatar dake akwai na’a zaɓi mutane masu ilmi da gogewa da cancanta.

“Har Shuwagabannin mu basu magance matsalolin tsaro, da talauci da rashin aikin yi, to wannan lokaci ne na canji. Bazamu taɓa bari a kawo mana mutanen da suka kashe ƙasa a jami’iyya domin su jagorance mu ba. Jam’iyyun siyasa dole su tabbatar da cewa akwai wasu matakai da zasu zaɓa waɗanda zasu yi shugabanci,” Inji Bugaje.

Labarai Makamanta

Leave a Reply