Jahadin Dake Kan ‘Yan Najeriya Shi Ne Kawar Da APC – Atiku

Dan takarar shugaban kasa na Babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya yi kira ga yan Najeriya da su fatattaki jam’iyyar All APC daga mulki a babban zaben 2023 mai zuwa domin dawo da Najeriya cikin hayyacinta.

Atiku ya yi wannan kira ne a ranar Lahadi, 12 ga watan Yuni, a cikin sakonsa na ranar dimokradiyya, yana mai cewa hakan shine babban jahadi kuma abin da za a iya sakawa jaruman dimokradiyyan kasar nan da shi.

Dan siyasar ya yi imanin cewa wannan bukin lokaci ne da dukkan masu kishin kasa za su hadu domin yin tunani da kuma aiki tare don hadin kan kasar, tsaro, daidaito, ci gaban al’umma da tattalin arziki da kuma ci gaban kasar baki daya.

Ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan damar wajen karfafa jajircewarsu kan sadaukarwar da magabata suka yi wajen karbo ‘yancin kan kasar.

A cewar tsohon mataimakin shugaban kasar, a bayyane yake cewa gwamnati mai ci ta kawowa al’ummar kasar cigaba mafi muni. Saboda haka, ya bukace su da su yi watsi da gwamnatin APC wacce ya bayyana a matsayin mara mutunci, mara farin jini, mara tunani kuma wacce bata san ya kamata ba.

Atiku ya jadadda cewa bai kamata a ba jam’iyyar da ta gaza cikawa mutane alkawaran da ta daukar masu game da tsaro, bunkasa tattalin arziki da yaki da rashawa damar sake yin wani wa’adi mara amfani ba.

Labarai Makamanta