Jagorancin Najeriya Ba Ya Tafiya Akan Tsari – Shugabannin Kudu

Kungiyar Shugabannin Kudanci da na Tsakiyar Najeriya ta ce hanya daya tilo da za a bi don kawar da mutuwar Najeriya ita ce a sake fasalin kasar, domin ceto ta daga barazanar wargajewa dake fuskantar ta.

Kungiyar a ranar Lahadi ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya yi wa ’yan Najeriya jawabi kan matsaloli daban-daban da kasar ke fuskanta. Edwin Clark, shugaban kungiyar na kasa, ya bayyana haka a wani taro daya gudana a birnin tarayya Abuja.

“Dalilin wannan taron a fili yake. Ina za mu je a Najeriya? Wasu na neman ballewa, wasu na neman tarwatsewa, wasu na tafiyar da tsarin mulki na bai daya, da sauransu.

“Lokaci yana tafiya cikin sauri kuma akwai bukatar mu bayyana matsayin mu karara ga ‘yan Najeriya. “Shugaban kasa ba sarki bane, ba jagora bane, ba sarkin gargajiya bane, dan siyasa ne. Ya kamata ya fito ya hadu da wasu daga cikinmu wadanda muke nan tun kafin ya kure.

“Kasar nan tamu ce gaba dayan mu, arewa kadai ko kudu kadai ba za su iya mulkin kasar nan ba. “Muna son sabon kundin tsarin mulki. Duk wani kwaskwarimar da za a yi wa kundin tsarin mulki, ba ni da kwarin gwiwa akansa.

“Mun zo nan ne don abubuwa biyu: Ya kamata a sake fasalta Najeriya. Shugaba Buhari ya taba cewa idan ba mu kashe rashawa ba, rashawa za ta kashe Najeriya.” “Na ce idan ba mu sake fasalin Najeriya ba za ta mutu.

Ballewa ba shine mafita ba. Abu na biyu, muna son tsarin shiyya-shiyya ya ci gaba. Tsarin mulki ne… muna son yankin kudu ya yi mulki a 2023.”

Yankin kudancin Najeriya na ci gaba da fuskantar hare-haren tsageru ‘yan bindiga a cikin ‘yan kwanakin nan. A makon da ya gabata, an kone ofisoshin ‘yan sanda da na hukumar zabe mai zaman kanta INEC da dama a yankin.

Labarai Makamanta