Izala Ta Fi Ta’addanci Da Garkuwa Da Mutane Muni – Ɗahiru Bauchi

Mashahurin Malamin Ɗarikar Tijjaniya a Najeriya Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, ya yi kira da babbar murya ga Fulani Makiyaya masu aikata ta’addanci da yin garkuwa da mutane cewa, su kula matuƙa akan halin da suke ciki, ka da akai ga matsayin da za su faɗa cikin Ƙungiyar Izala bayan ayyukan ta’addanci da suke yi, saboda munin Izala ya fi ta’addancin da suke ciki.

Shehin Malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi ga manema labarai dangane da halin da matsalar tsaro da ya addabi yankin Arewacin Najeriya wanda ake danganta matsalar akan Fulani dake rayuwa a daji.

Bauchi ya cigaba da cewar a tarihin ƙabilar Fulani Mutane ne Musulmi masu ƙaunar Manzon Allah, komai jahilcin Baffillatani zaka samu yana ƙaunar Manzon Allah, aikin ta’addanci da garkuwa da mutane wasu mutane ne suka sanya su ciki, bayan sun sace musu dukiyar su da Shanun su, amma kasancewar Fulani ba a san su da dukkanin wadannan miyagun abubuwa ba sai ya zamana nasu ya fitowa fili har ba’a ganin wadanda suka koya musu sai nasu kaɗai ake gani.

Sheikh Bauchi wanda ya siffanta halin ta’addanci da garkuwa da mutane a matsayin wani yanayi mai kama da rayuwa cikin taɓo, amma Izala tamkar rayuwa cikin kashi ne, saboda haka kada Fulani su yarda su shiga Izala domin ta fi ta’addanci da garkuwa da mutane muni.

Kalaman Sheikh Ɗahiru Bauchi na zuwa ne a daidai lokacin da sanannen malamin nan Dr. Ahmad Gumi ke kokarin shiga tsakani domin samar da yin sulhu tsakanin Gwamnati da Fulani ‘yan Bindiga.

Labarai Makamanta