Iya Taku Ya Sa Bamu Fallasa Masu Daukar Nauyin Ta’addanci Ba – Malami

Rahoton dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Antoni Janar na kasar nan kuma ministan sharia, Abubakar Malami (SAN) ya bayyana dalilan da yasa gwamnati ke jan kafa wajen fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Najeriya.

Malami, wanda ya zanta da kafar watsa labarai ta Channels TV a tsakiyar mako, yace ba wai gwamnatin tarayya ba ta son fallasa sunayen bane, tana jiran lokaci ne.

Wannan na zuwa ne duk da matsin lamba da kiraye-kiraye da ake wa shugaban kasa Buhari daga kowane ɓangare kan ya bayyana sunayen mutanen.

“Abu ɗaya da nake son ku fara duba wa shine har yanzun ana cigaba da bincike, kuma maganar gaskiya mun damke mutane da dama.” “Haka nan kuma mun samu umarnin cigaba da tsare mutanen da muka kama daga sashin shari’a.

Kuma babu adalci wani yace ba’a yi komai a kan wannan lamarin ba.” “Har yanzun muna kan bincike. Haka zamu cigaba da kasancewa muna bincike kuma tabbas zamu yi abinda ya dace a lokacin da ya dace.”

Ministan ya ƙara da cewa sunayen dake hannunsu ya kunshi yan cikin kasa da kuma sanannu da aka sani a kasashen duniya. Bugu da kari yace gwamnati ta damke su kuma ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen sauke nauyin da yan Najeriya suka dora mata.

Labarai Makamanta