Injiniyoyin Boko Haram Sun Yada Zango A Kaduna

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Shugabannin kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga Bakoura Buduma sun mayar da masu hada musu bama-bamai dazukan yankin kudancin Kaduna, a cewar wani rahoton da PRNigeria ta fitar.

A baya-bayan nan ne aka mayar da masu hada bama-baman da ake kira Amaliyyah a tsakiyar ‘yan ta’addan, dake hanyar Abuja zuwa Rijana, Igabi da Chikun a yankin hanyar kudancin Kaduna.

Majiyoyi daga ciki sun ce kungiyoyin biyu na Boko Haram za su yi amfani da duwatsun da ke yankin a matsayin mabuya domin kai hare hare.

A wani rahoton mai alaka da wannan, Kwamitin Shura na ISIS na shirin kawo wa shugabannin ISWAP ziyara, PRNigeria ta ruwaito daga majiyoyin masu tattara bayannan sirri.

An gano cewa, Abu Ibrahim al-Hashimi al-Quraishi, shugaban ISIS ne ya bada umurnin kai ziyarar a kokarin da kungiyar ke yi domin sake yi wa kungiyar garambawul.

Majiyoyi sun shaidawa PRNigeria cewa dalilin ziyarar na ISIS shine bada horaswa da kudade domin a dauki sabbin mayaka a yankin Afrika bayan rasa mayakansu da dama. Majiyar ta kara da cewa: “Za kuma su hada kai da ISWAP domin yakar yan ta’addan Boko Haram masu yi wa Bakoura biyayya.”

Labarai Makamanta