Inganta Shirye-Shirye: Kafafen Yaɗa Labarai Sun Bukaci DSTV/GOTV Da Basu Dama

Kungiyar masu kafafen yada labarai masu zaman kansu ta Arewacin kasar nan tayi kira ga hukumar dake kula da kafafen yada labarai ta kasa NBC umurci kanfanonin DSTV da GOTV su basu damar watsa shirye shiryen su kafafen nasu.


Shugaban kungiyar masu kafafen yada labarai masu zaman kansu a yankin arewacin kasar nan Alhaji Dakta Ahmed Tijjani Ramalan ne ya bayyana bukatar hakan sa’ilinda yake yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da Ministan yada labarai da Al’adu Lai Muhammad da mukaddashin shugaban hukumar NBC akan sabbin sauye sauyen da suka samar domin Inganta da kuma ci gaban kafafen yada labarai a kasar nan, ta yadda kafafen zasu yi gogayya takwarorin su na duniya.

Har ila yau kungiyar tasha Alwashin hada kai da hukumar NBC wurin ganin an aiwatar da dokokin dake cikin kuduri na 6 domin samun ci gaba mai dorewa

Labarai Makamanta