INEC Ta Yi Watsi Da Dan Takarar Sanatan APC A Akwa-Ibom

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta yi watsi da zaben fidda gwanin da ya samar da Godswill Akpabio a matsayin ‘dan takarar kujerar sanata Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma karkashin jam’iyyar APC.

Akpabio, wanda ya janye daga takarar shugabancin kasa yace a zabi Tinubu a zaben fidda gwanin APC, an bayyana shi matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na kujerar sanatan Akwa Ibom a ranar Alhamis.

Kamar yadda sakamakon sake zaben ya nuna, Akpabio ya yi nasara inda ya samu kuri’u 478, yayin da DIG Ekpo Udom, wanda ya lashe zaben a farko, ya samu kuri’u uku kacal.

Amma a yayin jawabi ga manema labarai a Uyo, babban birnin jihar a ranar Lahadi Mike Igini ya ce hukumar ta karbi wanda yayi nasara ne a zaben da INEC ta lura da shi. Ya musanta ikirarin cewa hukumar ta lura da sake zaben fidda gwanin, wanda Akpabio ya bayyana a matsayin mai nasara.

“An kammala zaben fidda gwanin a ranar 27 ga watan da ya gabata, don haka ban san abinda ku ke magana a kai ba. Wanda aka yi a baya shi ne wanda INEC ta lura da shi kuma tuni an aike da rahoton Abuja.

Labarai Makamanta