Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, a ranar Juma’a ta sanar da cewa ‘yan kasa da suka yi rijistar katin zabe kafin zuwan zaben 2023 zasu fara karba katin zabensu na dindindin daga ranar 12 ga watan Disamban 2022.
Wannan na kunshe ne a takardar da aka bai wa manema labarai a Abuja. Kamar yadda takardar tace, hukumar tayi taro a ranar Alhamis, 1 ga watan Disamban 2022 kuma suka tattauna kan wasu muhimman abubuwa da suka hada da fara karbar katinan zabe a fadin kasar nan.
An ruwaito tun da farko cewa, hukumar tayi taro a Legas da kwamishinonin zabe na jihohi 36 na fadin kasar nan daga 28 na watan Nuwamba zuwa 2 ga Disamban 2022.
A taron, hukumar ta kammala dukkan tsare-tsare tare da fitar da jadawalin karbar katinan zabe, takardar wacce ta samu sa hannun kwamishinan ilimantar da masu kada kuri’a, Festus Okoye, tace: “Hukumar ta saka Litinin, 12 ga watan Disamban 2022 zuwa ranar Lahadi, 22 ga watan Janairun 2023 a dukkan kananan hukumomi 774 na kasar nan.
“Hukumar ta yanke hukuncin bude wuraren rijistar zabe 8,809 na kananan hukumomin daga Juma’a 6 ga watan zuwa Lahadi, 15 ga watan Janairun 2022. “Wadanda basu samu damar karbar katinan zaben su ba a kananan hukumomin zasu iya wurin rijistarsu su karba.
You must log in to post a comment.