INEC Ta Kalubalanci Jami’anta Kan Zaben Abuja

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ƙalubalanci jami’an zaɓe na hukumar da ke ofishin ta na Gundumar Babban Birnin Tarayya da su tabbatar da cewa an cimma nasara a zaɓuɓɓukan da za a yi na ƙananan hukumomin yankin a ranar 12 ga Fabrairu.

Farfesa Yakubu ya faɗi haka ne a lokacin da ya kai ziyara ga jami’an zaɓe da sauran ma’aikatan INEC da ke ofishin hukumar na gundumar a garin Abuja a ranar Laraba inda su ka tattauna kan zaɓen da za a yi.

Yakubu ya ce ofishin INEC na yankin Abuja bai da wani uziri da zai iya ba ‘yan Nijeriya idan ya gaza cimma nasara, domin kuwa hedikwatar hukumar ta yi dukkan abin da ya kamata ta yi wa ofishin ta na gundumar domin gudanar da wannan zaɓe.

Ya bayyana fatan alherin cewa da yake akwai ƙwararrun jami’an zaɓe a ofishin INEC na gundumar waɗanda sun gudanar da zaɓuɓɓuka a baya, ba su da wani uziri da za su bayar a kan gudanar da wannan zaɓe na ƙananan hukumomin.

Ya ce, “Mun shata layin inganci wajen gudanar da karɓaɓɓen zaɓe a Nijeriya, don haka zaɓen gundumar Abuja ba zai kasa a hakan ba.

Labarai Makamanta