Inda Trump Ya Gayyaci Ganduje Da Bai Faɗi Zaɓe Ba – Doguwa

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Doguwa, ya ce tsohon shugaban Amurka Donald Trump ba zai iya faduwa zabe ba idan da ya nemi taimakon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.

Ado Doguwa, wanda ke wakiltar Mazabar Tudunwada/Doguwa, ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da aka turowa jaridar Daily Nigerian a ranar Laraba, yayin da yake yiwa magoya bayansa jawabi.

“Idan aka duba, lokacin da alkaluman suka fara nuna Trump zai sha kaye, ya kamata ya kira Ganduje a waya ya tura masa Murtala Garo ko Alhassan Ado ko Kawu Sumaila ko dan majalisa Kabiru Rurum da Labarin ba zai kasance haka ba a yau.

“A wurinmu, Ganduje cibiya ce ta siyasa. ‘Yan siyasa za su kwashe shekaru suna gaya muku karya game da cin zabe a 2023, kawai suna gaya muku shirme ne,” in ji Doguwa a cikin gajeren faifan.

Yawancin masu sa-ido masu zaman kansu suna da ra’ayin cewa jam’iyyar APC mai mulki tare da hadin gwiwar jami’an tsaro da manyan jami’an Hukumar Zabe ta Kasa mai zaman kanta, (INEC), sun yi magudi a zaben da aka yi a Maris 2019 don goyon bayan jam’iyya mai mulki.

Labarai Makamanta