Ina Tsoron Harkar Fim – Jarumi Zaharaddeen Sani


Fitaccen jarumi kuma Furodusa a masana’antar finafinai ta Kannywood wanda ya dade ana damawa da shi a cikin harkar, ya bayyana irin fargaba da kuma tsoron da ya ke da shi a game da ita masana’antar.

Jarumin ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da Dimukaradiyya ina ya ke cewa “ita harkar tana da daukaka mutum lokaci guda ya ji kamar ba za a daina yayin sa ba, sai ya ji kamar shi kadai ne. Ba ya tunanin an yi wasu kafin ya zo duka sun shude, sai dai abin ba ya zama izina ga na baya.”


Ya ci gaba da cewar “Gaskiya abin da na ke tsoro ya ke kuma tayar mini da hankali game da fim bai wuce tsoron jarumi a harkar fim. Domin harka ce wacce duk abin da ka yi ba za ka iya gamsar da mutane ba. Sannan ka na cikin tashen ka, sai ka ji wata rana ka zama tarihi, ba Wai sai ka mutu ba. Lokacin ka ne kawai ya wuce na wani ya shigo, don haka harkar fim abar tsoro ce. “.

Labarai Makamanta