Ina Kalubalantar El Rufa’i Ya Fito Da Dukiyarsa Ya Taimaki Talakawa – Me LA

Tsohon ‘dan takarar kujerar Majalisar dattawa mai wakiltan mazabar Kaduna ta tsakiya a jam’iyyar PDP, Hon Lawal Adamu Usman Mr LA ya jefawa gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Elrufai kalubale a inda ya kalubalance gwamnan da ya fito da dukiyar sa domin a tallafawa talakawan Jihar Kaduna dake fuskantar kalubalen rashin biyan kudin makarantar da Elrufai ya karawa yaransu da kuma tsananin rayuwar da talakawan Jihar ke fuskanta sakamakon takaita zurga zurga da gwamnatin Jihar Kaduna tayi na Hana hawa babur.

Mr LA ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da kashi na uku cikin Shirin tallafin kudin makaranta da ya ba daliban Jihar Kaduna na naira miliyan 50.

Tun a farko dai matashin ‘dan siyasan ya fito da tallafin zunzurutun kudi naira miliyan 30 domin ya saukake wa yaran marasa karfi a fadin Jihar Kaduna sakamakon Karin kudin makaranta da gwamnan Jihar Kaduna yayi. Amman biyo bayan Yadda aka turo da bukatun dalibai wanda hakan yaga kudin da ya fito dasu ba zasu Isa ba yasa a watan satunbar data gabata ya kara miliyan 20 akai ya koma naira miliyan hamsin kuma gidauniyar a halin yanzu tana sa ran Biyawa dalibai 400 daga manyan makarantun jihar Kaduna.

Mr LA yace “shima El Rufa’i a matsayinsa na ‘dan Jihar Kaduna Wanda Jihar ke biya albashi yana Kalubalantar sa daya fito da kudi domin a hadu a bunkasa Rayuwar matasan Jihar Kaduna, domin idan aka bar matasan mu Babu ilimi tamkar an lalata rayuwarsu ne. Mr LA ya kara da cewa irin su Elrufai kyauta sukayi karatu a baya, dan Haka meye dalilinsu na Kara kudin karatu idan har suna so dan talaka ya samu Ilimi kamar yadda suka samu?

Daga karshe ya shawarci gwamnan Jihar Kaduna da ya bullo dawani hanyar da zai ragewa talakawan Jihar Kaduna saukin radadin rashin babur da ya haramta hawa a Kaduna.

Labarai Makamanta