Ina Goyon Bayan Tsarin Karba-Karba – Shehu Sani

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar tsohon dan majalisa da ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani, ya goyi bayan mulkin karba-karba don adalci samun da daidaito.

Ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da Gidan Talabijin na Channels yayi da shi ranar Talata dangane da batun siyasar Najeriya a lokacin da shekarar zaɓe ta 2023 ke ƙara tinkarowa.

Ra’ayin Sanatan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta muhawara kan wanda zai gaji Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda zai kammala wa’adin mulkinsa na biyu a shekara mai zuwa.

“Abu mai yiwuwa ne mulkin karba-karba, abu mai yiwuwa ne tabbatar da ganin cewa dukka yankunan kasar sun samar da shugaban kasa; amma za a iya cimma haka ne ta hanyar fahimtar juna tunda baya a kundin tsarin mulki.

“Shugabannin siyasa a arewa, gwamnoni da sauransu na iya zama da shugabannin siyasa daga kudancin kasar sannan suce ya kamata mu yarda a wannnan dandamali sannan mu cimma haka. Yin hakan abu mai yiwuwa ne.

“Babu wani bangare na kasar da zai iya samar da Shugaban kasa ba tare da dayan bangaren kasar ba. Shugaba Buhari ya gwada sa’arsa a 2003, 2007, 2011 don ganin ya zama Shugaban Najeriya, amma bai yi nasara ba har sai da ya hada kansa da kudu maso yamma, da mutane irin su Tinubu da sauransu.”

Labarai Makamanta