Ina Goyon Bayan Hukuncin Kisa Kan Makashin Hanifa – Aisha Buhari

Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Uwar gidan shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari, ta shiga jerin yan Najeriya dake kiran a ɗauki tsattsauran mataki kan makasan Hanifa Abubakar.

Hanifa Abubakar ‘yar kaminin shekara 5 a duniya, ta rasa ranta ne a hannun shugaban makarantarsu, wanda ya yi garkuwa da ita kuma ya kashe ta sannan ya binne gawarta a wani wuri cikin Makarantar.

Uwargidan shugaban ƙasa ta sanya wani gajeren bidiyo a shafinta na Instagram, wanda babban malamin addninin musulunci, Sheikh Abdallah Gadon ƙaya, yake neman a ɗauki mataki kan lamarin.

A cikin kalamansa, Malamin yace ran makashin Hanifa bai fi na wacce ya kashe ba, dan haka shi ma a kashe shi kowa ya gani domin zama darasi ga ‘yan baya.

Gadon Ƙaya yace: “Don haka kamata ya yi a kashe shi, kamar yadda ya halaka ƙaramar yarinya. Kuma idan za’a kashe shi, kamata ya yi a fito fili kowa ya gani, domin gobe kar wani ya maimaita.”

Aisha Buhari ta nuna goyon bayanta kan kalaman malamin na raba makashin Hanifa da duniya, kuma ta jawo hankalin sufeta janar na yan sandan ƙasar nan. A kalamanta, uwar gidan shugaban ƙasa tace, “Muna goyon bayan hukuncin kisa kan Malamin.”

A ranar 2 ga watan Disamba, 2021, shugaban makarantar yara dake Kwanar Dakata, ƙaramar hukumar Nasarawa, cikin kwaryar birnin Kano, Abdulmalik Tanko, ya sace Hanifa Abubakar.

Jami’an tsaro sun samu nasarar kame Tanko, wanda ya karbi N100,000 a wani sashi na miliyan N6m da ya nema kudin fansa daga iyalan yarinyar. Shugaban makarantar ya kashe ƙaramar yarinyar da maganin ɓera na N100 kacal, kamar yadda ya tabbatar wa hukumar ‘yan sanda.

Labarai Makamanta