Ina Da Wani Buri Kafin Aure – Jaruma Ummi Gombe


“Na samu shekaru masu yawa Ina cikin harkar fim sai dai ban samu damar dana samu ba sai a wannan lokacin, don haka na ke ganin a yanzu na zama cikakkiyar Jarumar da ba zan yi shakkar kowa ba.”

Jaruma Hadiza Abubakar wadda aka fi sani da Ummi Gombe a Masana’antar Kannywwod ce ta bayyana hakan a lokacin tattaunawar su da Dimukaradiyya.

Ta ci gaba da cewa” kamar yadda sauran Jarumai masu aji su ke ji da Kan su to nima a yanzu jaruma ce mai aji don haka a yanzu lokaci na ne da Allah ya kawo a ke damawa da ni. “

Sai dai mun tambaye ta ko wanne buri take da shi nan gaba”

Sai ta ce ” a nan gaba Ina da burin samar da wata harkar kasuwancin da zan rike kaina ko da kuwa na yi aure ne, domin ka san mu mata rayuwar mu gajeriya ce, sai ka ji an ce mun yi aure, don haka Ina fatan Allah ya cika mini burina na zama babbar yar kasuwa kafin lokacin da zan yi aure, Kuma Ina fatan Allah ya kawo mini mijin aure wanda zai rike ni tsakani da Allah da ni da yaran da zamu haifa. “

Labarai Makamanta