Ina Da Tabbacin Buhari Zai Magance Matsalar Tsaron Najeriya – Jonathan

Tsohon Shugaban ƙasa Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana cewar, yana da kyakkyawar fata da kuma yaƙini akan Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai shawo kai tare magance matsalar tsaro wadda ta daɗe tana ci wa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya.

Goodluck Ebele Jonathan ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya hada kai da gwamnoni, shugabanni tsaro da sauran masu ruwa da tsaki wurin shawo kan matsalar tsaron kasar nan.

Jonathan yayi wannan furucin ne yayin da ya jagoranci wasu wakilan siyasa daga Jihar Bayelsa zuwa ta’aziyya ga Gwamna Ifeanyi Okowa a gidan gwamnatin Asaba na jihar Delta a kan rasuwar mahaifin gwamnan.

Ya ce abin takaici ne yadda ake sace yaran makarantu da sauran ‘yan Najeriya, da yadda ‘yan Bindiga ke yin yadda suka ga dama a arewacin Najeriya.

“Ina da tabbacin idan gwamnoni da gwamnatin tarayya suka mayar da hankali, zamu iya shawo kan matsalar rashin tsaro a kasar nan. “Ina da tabbacin shugaban kasa baya bacci kuma gwamnonin kasar nan basu bacci a kan kalubalen tsaron kasar nan.

“Matukar gwamnoni, shugaban kasa da dukkan hukumomin tsaro za su yi aiki tare, Najeriya za ta iya tsallake wannan mummunan kalubalen da take fuskanta,”.

A yayin jinjinawa shugaban kasa a kan kokarinsa na shawo kan matsalar tsaro, Jonathan ya bayyana tabbacin da yake da shi akan Buhari, sannan ya bukaci ‘yan Najeriya da su hada karfi da karfe wurin fatattakar rashin tsaro.

Labarai Makamanta