Ina Da Cikakkiyar Lafiya Ta Jagorar Najeriya – Tinubu

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC mai mulki Bola Ahmed Tinubu, ya musanta zargin da ake yi cewa ba shi da lafiya, yana mai cewa “ban janye daga takara ba”.

Wani bidiyo da dattijon mai shekara 70 ya wallafa a shafinsa na Twitter ya nuna shi yana motsa jiki a kan keke, har ma yana cewa “a shirye nake na fara mulkin Najeriya daga ranar farko”.

“Wasu da yawa na cewa na mutu; wasu sun yi iƙirarin na janye daga takara,” a cewarsa. “To…ba haka ba ne.”

Ya ƙara da cewa: “Ga gaskiyar lamarin: Garau nake, da lafiyata kuma a shirye nake na fara mulkin Najeriya daga ranar farko.”

Wannan ne karon farko da aka ji daga Tinubu tun bayan da ya fice daga Najeriya tsawon lokaci, inda abokin takararsa Kashim Shetttima ya dinga wakiltarsa a wurin taruka.

A ranar Laraba ne aka ƙaddamar da kamfe a hukumance yayin da Tinubu ke shirin fafatawa da Atiku Abubakar na babbar jam’iyyar adawa ta PDP da sauran ‘yan takara 14 a zaɓen shugaban ƙasa na watan Fabarairu mai zuwa.

Labarai Makamanta