Ina Alfahari Da Masoyana – Jaruma Hafsat Hassan


Wata Sabuwar jaruma a Masana’antar Kannywwod Hafsat Hassan ta nuna yadda take jin dadin ta a game da irin kaunar da mutune su ke nuna Mata tun daga lokacin da suka fara ganin ta a cikin shirin fim.

Jarumar ta bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da Jaridar Dimukaradiyya da muka tambaye ta irin yadda ta ke gudanar da rayuwar ta a matsayin ta na Sabuwar jaruma sai ta ke cewa.

“To a gaskiya duk da ban dade da fara shirin fim ba, Ina alfahari da ita saboda alamun nasara da na ke gani, domin ni ka ga a baya Ina rayuwata komai babu wani da zai yi magana ta, Amma a yanzu ko Unguwa zan tafi dole sai na rufe fuskanta, saboda idan ban yi Hakan ba, sai mutune su yi ta Kira na suna tsayar da ni saboda sun ganni a fim to duk da abin yana damu na Ina son Hakan.

Sannan Kuma idan muka shiga cikin jama’a sai ka ga kowa yana son ya gan ka ya yi Hoto da Kai to Ina jin dadin Hakan domin ka zama wani a cikin mutane da za a rinka kallon ka ana kaunar ka ai abin so ne don haka sai dai fatan Allah ya sa na fi Hakan anan gaba.”

Daga karshe ta yi fatan Allah ya sa ta gama da shirin harkar fim lafiya.

Labarai Makamanta