Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana fatansa na cewa kada wani abu ya zo ya hana zaben watan Fabrairu da Maris masu zuwa. Obasanjo Yayi Bayani kan Zargin Yadda Ake Kokarin Hana Yin Zaben 2023.
Obasanjo ya bayyana damuwarsa kan zabukan yayin da mambobin kwamitin yardadda na jam’iyyar ADC suka ziyarcesa a gidansa da ke Abeokuta, jihar Ogun.
Tsohon shugaban kasar ya sanar da hakan ne sakamakon halin da ‘yan kasar nan ke cikin saboda rashin takardun sabbin kudi da man fetur wanda ka iya sa dole a dage zaben.
“Muna cikin wani hali a Najeriya, kasa da makonni uku za a yi zabe. Toh ina fatan babu abinda zai hana hakan. A kasa da makonni uku, za mu zabi shugaban da zai karba ragamar Najeriya na tsawon shekaru hudu. “Dukkanmu da ke Najeriya, kamar yadda na fadi da safen nan, na je Togo, Ghana da Cote d’Ivoire daga farko makon nan kuma sun damu da abinda ke faruwa a Najeriya.”
Obasanjo yace dole ne ‘yan Najeriya su yi duk abinda ya dace don ganin an yi zaben kamar yadda aka tsara. Ya kara da cewa, duniya ta matukar mayar da hankali wurin ganin cewa Najeriya tayi zabenta lokacin da ta tsara,
You must log in to post a comment.