Ilimi: Za A Fitar Da Dalibai 6000 Kasar Waje – Gwamnatin Tarayya

Hukumar kula da asususn cigaban kimiyya ta Najeriya, PTDF, ta fara tantance kimanin dalibai 6,000 da suke neman guraben samun tallafin karatu daga gwamnatin tarayya a jami’o’in kasashen waje na shekarar 2020/2021 kamar yadda Legit ta ruwaito.

A cewar hukumar, fiye da mutane 25,000 ne suka nemi guraben samun tallafin a matakin digiri na biyu Msc da kuma PhD, daga cikinsu ne hukumar ta ware mutane 6,000 wadanda za ta yi ma tamyoyin gaba da gaba da kuma tantancewa.

Shugaban sashin tallafin karatu na kasashen waje, Bello Mustapha ya bayyana cewa za su dauki tsawon makonni biyu suna gudanar da aikin tantancewar a dukkanin shiyyoyin Najeriya guda shida.

“Muna amfani da kashi 90 na tsofaffin daliban da muka dauki nauyinsu a matakin PhD, kuma suka samu kyawawan sakamako a matsayin wadanda za su yi ma masu neman guraben tambayoyi, ire iren mutanen sun kai 91 da muka dauka don yin wannan aiki.” Inji shi.

Daga cikin kasashen da gwamnatin Najeriya ta kulla alakar fitar da dalibanta zuwa jami’o’insu akwai Farasa, Jamus, China, Birtaniya da kuma kasar Malaysia.

Related posts