Ilimi Ne Babban Jagora A Aikin Agaji – Shugaban ‘Yan Agajin Fityanul Islam

Daga Muhammad Sani Yusuf Nassarawa

An bukaci ‘Yan Agajin Munazzamutul FItyanul Islam Su Kara Himma akan Aikinsu na Taimakawa Addini ta Kowacce Fuska ta Hanyar Samun Ilimin Aikin Agajin Wanda Shine Jagora.

Wannan Kira ya Fitone daga Bakin Babban Kwamandan ‘Yan Agajin Babban Birnin Tarayya Abuja, Alhaji Yakubu Abubakar a Lokacin da Kungiyar ta Shirya Taron da ta Saba Gudanarwa na Karshen Shekara.

Taron Wanda ya Gudana a Unguwar Daki Biyu dake Jabi Abuja ya Samu Halartar Shugabannin ‘Yan Agaji Daga Dukkan Kananan Hukumomin Babban Birnin na Abuja.

Tunda Farko a nasa Jawabin Kwamandan ‘Yan Agajin Munazzamatu Daga Jihar Kogi Barista Muhammad Suraj Yusuf Lokoja ya Gargadi ‘Yan Agajin akan Maida Hankali akan Karatu Wanda Shine Mabudin Dukkan Alkhairi.

Daga Karshe Alhaji Yakubu Abubakar Kwamandan Agajin na Abuja Karkashin Kungiyar Munazzamatu Fityanul Islam yaja Hankalin ‘Ya’Yan Kungiyar su Zama Masu Sanya Ido Sosai Wajen Bada tasu Gudumawa akan Tsaron Nijeriya da Zaman Lafiya Baki Daya, Inda Yace da Zarar Sunga Abinda basu Yarda da shi ba Suyi Gaugawar kai Rahoto ga Jami’an Tsaro Mafi Kusa.

Taron ya Karkare da Karawa Wasu Jami’an Kungitar Karin Girma na Mukamin Jami’an Ladabtarwa.

Labarai Makamanta