Ilimi Kanawa Ke Buƙata Ba Gada Ba – Martanin Kwankwaso Ga Ganduje

Tsohon Gwamnan Jihar Kano mai girma Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya soki lamirin Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje game da shirin da gwamnatinsa ke yi na ciyo bashin naira biliyan 20 domin aiwatar da aikin gina gada a birnin jihar.

A cewar Kwankwaso, hakan ba daidai bane ga gwamnati ta ciyo bashin da zai bar al’ummar da za a haifo nan gaba da gwagwarmayar biyan bashi, a maimakon haka ya kamata a yi abin da ya dace ne musamman haɓaka Ilimi a jihar.

A wata hira da yayi da sashin hausa na BBC, tsohon gwamnan ya ce gina gadar wadda ta hada birnin Kano da hanyar zuwa Wudil, hakki ne da ya rataya a kan wuyan gwamnatin tarayya ba jihar ba.

“Maimakon a ce gwamna ya je ya ga Buhari domin ya fada masa cewa ‘ka zo ka yi mana gada’, hakan bai yi ba, gadojin da muka yi a Kano gaba dayansu da kudin gwamnatin wannan lokaci muka yi su.”

Kwankwaso ya kara da cewa duk da ana bukatar gada a Kano, amma abin da mutanen jihar suka fi bukata shi ne ilimi . “A koya wa yayan talakawa sana’oi na hannu wanda yara za su iya rike kansu”, in ji shi.

Har la yau, ya soki yadda gwamna Ganduje yake sayar da filaye lamarin da ya haddasa cece-kuce a baya-bayan nan.

Da yake magana kan makomar filayen da gwamnatin Kano ke sayarwa kuwa, Kwankwaso ya bayyana cewa matukar mulki ya koma hannunsu, to ba makawa sai an rushe gine-ginen da aka aza kan filayen.

Ya ce: “Duk wani gurin hukuma, mutum ko ya yi bene hawa dubu a ruguzo shi, a share gurin a mayar da shi yadda yake da.”

Labarai Makamanta