Ilimi: Gwamnatin Gombe Ta Yi Rawar Gani – Kwamared Sabo

Tsohon Shugaban Kungiyar ɗalibai ‘yan asalin jihar Gombe na kasa Kwamared Sani Sabo yace nasarorin da gwamnatin jihar ta ke samu a bangaren ilimi musamman ma wurin gina ƙarin sabbin azuzuwa domin samar da kyakyawan yanayin koyon karatu abu ne dake inganta ilimi daga tushe.

Kwamared Sani Sabo wanda ke tsokaci akan bunƙasar ilimi a jihar a hirarshi da wakilinmu, yace an samu cigaba matuka a bangaren ilimi daga tushe a jihar lura da gina sabbin azuzuwa da dalibai ke shiga suyi karatu a natse, musamman a yankunan karkara.

Kwamared Sabo ya ƙara da cewa ayyana dokar ta baci akan ilimi da gwamnatin jihar Gombe tayi yana samar da kyawawan sakamako dake bukatar al’umma a jihar su cigaba da bada goyon baya ga gwamnatin a kokarin ta na kai jihar kololuwar cigaba da samun cigaban ilimi mai dorewa.

Labarai Makamanta