Idan Sanya Hijabi Zai Kare Mata Daga Harsashi Muna Goyon Baya – CAN

Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN ta ce ta yarda Sojoji mata da jami’an tsaro mata Musulmi su sanya Hijabi muddin zai karesu daga harsashin bindiga a filin daga.

Sakatare Janar na kungiyar CAN, Joseph Daramola, ya bayyana hakan a hirar da yayi da manema labarai ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja.

Daramola ya yi tsokaci ne kan dokar da ake shirin kafawa a majalisar wakilai da zai hallatawa Sojoji mata Musulmi sanya Hijabi.

Mataimakin shugaban kwamitin kudi na majalisar kuma mai wakiltar mazabun Bida/Gbako/Katcha, Saidu Abdullahi, ne ya gabatar da wannan kudiri.

Sashe na 13 na kudirin yace, “Dokar za ta haramta nuna bangaranci lokacin daukan aiki don mace ta sanya Hijabi.”

Sakataren Kungiyar CAN ɗin ya ƙara da cewa a kasashe irinsu Bida/Gbako/Katcha, matansu na sanya Hijabi saboda haka ba matsala bane da ya kamata ya dauke hankalin ‘yan majalisa daga abubuwa masu muhimmanci irinsu tsaro da tattalin arziki.

Daramola yace, “Idan suka ga dama su sanya yar siket ko babbar riga. Idan Hijabin zai karesu daga harsashi, su sanya, tun da abinda suke so kenan.”

Labarai Makamanta