Idan Muka Fallasa Masu Ɗaukar Nauyin ‘Yan Bindiga Kowa Sai Ya Firgita – Buhari

Fadar Shugaban kasa ta ce gwamnatin tarayya ta gano wadanda ke daukar nauyin Boko Haram da ‘yanbinda da zai girgiza jama’a.

Fadar, ta ce akwai alaka tsakanin masu daukar nauyin masu satar jama’a, ‘yanbindiga da kuma Boko Haram.

A cewar mai Magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mallam Garba Shehu, daga cikin masu daukar nauyin ‘yanta’addar, akwai ‘yan kasuwar musayar kudi da ke da jama’a a kasashen waje.

Ya ce akwai shaidar da ke tabbatar da ana turo kudi daga Hadaddiyar Daular Larabawa, zuwa ga shugabannin kungiyar Boko Haram.

Shehu ya tabbatar da cewa, ikirarin da shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya Kayode Fayemi ya yi na cewa masu daukar nauyin Boko Haram ke kitsa ayyukan ‘yanbindiga da satar mutane bayanai ne na sirri da aka samar.

Ya ce an kama mutane da dama kan wannan matsalar, kuma za a gurfanar da su da zaran an gama bincike, yana mai cewa babu wanda zai sha a cikinsu, ko da kuwa daga cikin wadanda binciken zai shafa akwai ‘yan siyasa.

Labarai Makamanta