Hukumar Zaɓe Ta Ayyana Ranar Cigaba Da Rijistar Masu Zabe

Hukumar Zabe mai Zaman Kan ta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa za a ci gaba da aikin rajistar katin masu zabe a ranar 28 ga watan Yunin wannan shekara ta 2021.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a taron da ya yi da su a hedikwatar hukumar a Abuja a ranar Alhamis.

“Bayan mun duba wadannan matsaloli da matakan da mu ka dauka don magance su, yanzu hukumar ta kai matsayin da za ta iya bayyana Litinin, 28 ga Yuni, 2021 a matsayin ranar da za mu koma mu ci gaba da rajistar katin zabe (CVR) a duk fadin kasar nan.”

Ya ce za a ci gaba da gudanar da aikin har zuwa kashi na uku na shekarar 2022.

Wannan aiki, kamar yadda aka tsara a Sashe na 10 na kundin Tsarin Mulkin Nijeriya, za a ci gaba da yin sa babu yankewa to amma hakan ba ta yiwu ba saboda “matsalolin rashin abin hannu.”

Yakubu ya ce ba a iya ci gaba da aikin ba ne yawanci saboda matsalar nan ta cutar korona (COVID-19).

Ya ce: “Abin da ya biyo bayan Babban Zaben kuma kamar yadda aka saba yi shi ne al’amura daban-daban na hukumar, kamar su shari’un bayan zabe, nazarin bayan zabe, da kuma zabubbukan da ba su cikin tsari daban-daban, musamman zabubbukan gwamna a jihohin Kogi da Bayelsa, wadanda aka yi a karshen 2019.

“Irin wadannan zabubbukan tilas ne a gudanar da su tare da yin amfani da Rajistar Masu Zabe da aka yi amfani da ita a Babban Zaben 2019.

“An kasa ci gaba da aikin CVR a cikin 2020 yawanci saboda annobar korona. Don bin shawarar da jami’an kiwon lafiya su ka ba kowa a kan tarurrukan da ake hada gungun mutane masu yawa, mun yanke shawarar cewa bai dace a ci gaba da aikin CVR ba a daidai lokacin da ake kan kololuwar annobar.

“Hukumar ta fitar da cikakken tsari kan yadda za a gudanar da zabubbukan a lokacin annobar korona, wanda ya maida hankali ga yin zabe da ya dace, tunda dai tilas ne a yi zabubbukan don kauce wa duk wani rikicin saba wa kundin tsarin mulki da za a danganta shi da karewar wa’adin mulki. An yi irin wadannan zabubbukan a jihohin Edo da Ondo a karshen shekarar da ta gabata.

“Tunanin mu a lokacin shi ne a farkon shigowar wannan shekara za mu samu damar kammala dukkan zabubbukan da su ka rage, wadanda ba su cikin kakar zabe kuma annobar korona za ta ragu.

“Kuma a lokacin mu na bukatar lokacin da za mu sanya sababbin tsare-tsare da za su taimaka a yi aikin rajistar masu zabe cikin kare lafiya idan annobar ta ci gaba da wanzuwa.”

Shugaban na INEC ya ce da farko an tsara cewa za a fara ci gaba da aikin ne a cikin wata uku na farkon shekarar 2021.

Yakubu ya ce yanzu dai hukumar ta gama shirin soma aikin a ranar 28 ga Yuni kafin a yi zaben gwamnan Anambra na shekarar 2012.

Ya ce za a yi shekara daya ana aikin har zuwa cikin kashi na uku na 2022 tare da maida hankali kan Jihar Anambra saboda zaben gwamnan jihar wanda za a yi a ranar 6 ga Nuwamba.

Ya ce, “Daga ranar Litinin, 28 ga Yuni, 2021, za a fara aikin CVR a duk fadin kasar nan kuma za a dinga yin sa ba tsayawa har sama da shekara daya, har zuwa cikin kashi na uku na 2022.

“Domin a kammala shirye-shiryen zaben gwamnan, za a dan dage aikin CVR a jihar a cikin Agusta 2021. Hakan zai ba hukumar damar ta share bayanan jihar sannan ta buga katittikan zabe saboda masu yin rajista.

Yakubu ya kuma bayyana cewa injin da ake amfani da shi a da ana tantance mai zabe wanda ake kira ‘Direct Data Capturing Machine’ (DDC), yanzu za a maye gurbin sa ne da wasu kananan na’urorin komfuta don samun karin sauki a lokacin zabe.

Sabuwar na’urar ana kiran ta ‘INEC Voter Enrolment Device’ (IVED) kuma an yi ta ne bisa tsarin karamar komfutar ‘tablet’ mai aiki da tsarin Android.

Labarai Makamanta