Hukumar da ke yaki da almundahana da sauran lafukan da suka shafi cin hanci ta ICPC ta ce ta rufe jami’o’i da kwalejin kimiyya da fasaha da ke bayar da shaidar digiri na bogi 62 a fadin kasar.
Hukumar ta ce wannan abu ne da ke neman zama ruwan dare a Najeriya, domin kuwa babu wata jiha a fadin kasar da ba a samu irin wannan makarantu ba a cikinta.
Cikin shekaru da ICPC ta kwashe tana gudanar da wani bincike a boye, ta kai ga gano adadin makarantu da suka hada da jami’o’i da kwaleji-kwaleji 62 na bogi da ke bayar da shaidar digiri a fadin Najeriya.
Amma ta ce an fi samun irin wadannan makarantu a arewa ta tsakiyar Najeriya.
Hukumar ICPC ta ce ta bayyana wannan gagagrumar barna ne, domin shaida wa ‘yan Najeriya cewa tana kallon duk wani mai shirin yin al-mundahana a kowanne fanni.
Ta ce ko da za a dauke kai a ko ina, to ba dai a bangaren ilimi ba, domin kuwa duk kasar da ba ta da tsarin ilimi ingantacce, to gobenta za ta iya kasancewa cikin kila wa kala.
Muhammad Ashiru Baba shi ne shugaban sashen wayar da kan jama’a na hukumar ICPC, ya kuma ce abin takaici ne halin da ilimi ya tsinci kansa a Najeriya.
Ya kara da cewa ”mafi yawan Jami’o’in ba su da ginin kansu, a maimakon haka suna amfani da gine-ginen Sakandire da na Furamaren da ba a karatu a karshen mako domin gudanar da karatunsu, kuma cikin shekara guda mutum zai samu shaidarsa”.
Wanda hakan ke nufin iyayen da suke kai yaransu irin wadannan wurare, sun kwana da sanin inda suke kai yaran nasu ba wajen kwarai ba ne.
Ashiru Baba ya ce a kwanakin baya har kama sansanin ‘yan bautar kasa suka yi na boge, wani abu da suka jima yana daure musu kai.
ICPC ta cimma nasarar kulle wadannan jami’o’i ne ta hanyar bayanai da ta samu daga hukumar da ke kula da Jami’o’i ta Najeriya NUC, kuma tun daga 2016 take gudanar da wannan aiki har ya zuwa yau.
You must log in to post a comment.