Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Bankado Tufka Da Warwara 257 A Kasafin 2021

Rahotanni daga Abuja babban birnin tarayyar Najeriya na bayyana cewa Shugaban Hukumar Yaƙi da Almundahana a Ma’aikatun Gwamnati (ICPC), Bolaji Owasanoye ya bayyana cewa ICPC ta bi diddigin kasafin kuɗi na 2021, inda ta gano akwai wuru-wurun maimanta sunayen ayyuka sau biyu har ayyuka 257 a cikin Kasafin Kuɗaɗe na 2021.

Bolaji ya ce ICPC ta gano wannan mummunar harƙalla ce bayan ta yi wa kasafin filla-filla.

Ya ce adadin kuɗaɗen da aka dafkara a cikin kasafin za su kai naira biliyan 20.138.

Bolaji ya zargi ma’aikatun da ministoci daban-daban ke jagoranta da kuma sauran hukumomin gwamnati da satar maƙudan kuɗaɗe ta hanyar cushe a cikin kasafin kuɗi, danƙara sunayen ma’aikatan bogi da kuma sauran laifukan zamba.

Labarai Makamanta