Hukumar NCDC Ta Kaddamar Da Sashin Binciken Cututtuka A Ebonyi

Shugaban Hukumar hana yaɗuwar cututtuka ta kasa Dr. Chile Ihekweazu ya kaddamar da sashin bincike da daƙile cututtuka a jami’ar koyarwa ta Alex Ekweume dake Abakaliki a ranar Talata.

Sashin binciken dai hukumar hana yaɗuwar cututtuka NCDC ce ta gina shi da haɗin gwiwar ma’aikatar lafiya ta tarayya, wanda aka samar dashi a cibiyar bincike da magance cututtuka dake jami’ar.

Dr. Ihekweazu a yayin kaddamarwan ya kalubalanci ma’aikatan asibitin koyarwar da yin dukkanin mai yiwuwa wajen wajen kula da sashin.
Sannan ya shawarce su da cigaba da kula da sashin binciken yadda ya kamata ta yadda zai zamo wata cibiyar binciken da magance cututtuka a fadin Nijeriya.

A lokacin da yake mayar da jawabi Shugaban Kwamitin gudanarwa na jami’ar Dr. Alhaji Tijjani Ramalan, ya bayyana samar da sashin binciken a matsayin wani babban al’amari da zai taimaka wajen inganta ayyukan bincike da magance cututtuka a faɗin Najeriya.

Ramalan ya kara da cewar Sashin binciken zai daga darajar asibitin zuwa wani babban mataki a idon duniya a matsayin wurin da za’a rinƙa ziyara domin gudanar da ayyukan bincike akan cututtuka.

Anashi ɓangaren babban daraktan Lafiya na Asibitin Dr. Emeka Onwe Ogah, ya yaba wa Hukumar NCDC bisa ga gudummuwa da taimakon da take ba asibitin, musanman wannan gagarumin aikin da ta yi na gina sasshin binciken.

Dr. Ogah ya kuma yaba gami da jinjina ga shugaban ƙasa Buhari bisa ga kulawa da goyon baya da yake ba hukumar asibitin wajen gudanar da muhimman ayyukan ta.

Labarai Makamanta