Hukumar Kwastam Na Hankoron Tara Tiriliyan Biyu A Badi

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar kwastam mai yaki da masu fasa-kauri tana shirin samun Naira tiriliyan biyu a matsayin kudin shigar gwamnati a shekara mai zuwa.

Rahoton ya bayyana cewa mafi yawan wannan kudi za su fito ne daga iyakokin da ake da su a yankin kudu maso yammacin Najeriya, ana sa ran iyakokin Legas, Ogun, Ondo da kuma jihar Oyo za su kawo kashi 80% na kudin.

Alkaluman da aka samu daga hukumar kwastam sun nuna jihohin nan hudu ne ke da alhakin kashi 80.48% na kudin shigan. Jihohin sun yi iyaka da tekun Benin.

Abin da rahoton 2022 ya kunsa “Alkaluman sun nuna daga cikin Naira tiriliyan 2 da za a samu a shekarar, Naira tiriliyan 1.6 za su fito ne daga yankin Kudu maso yamma.”

“Naira biliyan 264.2 daga yankin kudu maso kudu, da Naira biliyan 36.53 daga kudu maso gabas.” “NCS tana sa ran samun Naira biliyan 35.35 daga Arewa maso yamma, Naira biliyan 20.21, sai Naira miliyan 662 daga Arewa maso gabas.”

Jihohin Kudu maso yamma za su fito da 81% Abin da hukumar za ta samu daga Legas kadai ya kai 75%, yayin da Ogun, Ondo, da jihar Oyo za su bada gudumuwar kusan 5% daga ofisoshi 14 da ke yankin.

Harajin da kwastam take samu ya kasu ne tsakanin iyakokin Apapa (30.359%), PTML (11.911%), Tin Can (25.367%), da kuma dayan iyakar Tin Can II (1.143%). Sai iyakar Kirikiri (1.502%) da na Lagos Industrial (1.065%).

Gwamnatin Tarayya tana samun kudi a tashar jirgin sama na Murtala Muhammad da iyakar Seme Abin da ake samu a Arewa maso tsakiya da Arewa maso yamma bai kai 3% ba. Harajin da ke shigowa Najeriya ta iyakokin Arewa maso gabas bai kai 1% ba.

Labarai Makamanta