Hukumar INEC Ta Soke Rijistar Zabe Miliyan Uku

Hukumar zaɓe ta ƙasa ta ce kashi 40 cikin 100 na sabbin waɗanda ta yi wa rajistar katin jefa ƙuri’a ɗalibai ne, tana mai cewa ta soke rajista kusan miliyan uku da suka saɓa wa ƙai’dojin hukumar.

Shugaban hukumar ta Independent National Electoral Commission (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu ya ƙara da cewa kashi 76 cikin 100 na masu zaɓe a ƙasar matasa ne.

A cewarsa yayin wani taro da jam’iyyun siyasa a Abuja ranar Laraba, an samu ƙarin masu katin jefa ƙuri’a 9,518,188 a kan 84,004,084 da ake da su, kuma a yanzu rajistar farko-farko ta nuna cewa jimillar adadinsu ya kai 93,522,272.

“Bayan kammala aikin, mutum 12,298,944 ne suka yi rajistar. Amma tun tuni mun sha faɗa cewa hanyoyinmu na tsaftace rajistar masu inganci ne,” in ji shi.

“Bayan mun tantance bayanan ta hanyar amfani da tsarin Automated Biometric Identification System (ABIS), mun gano 2,780,756 (kashi 22.6 cikin 100) ba su cancanta ba kuma muka goge su. Cikinsu akwai waɗanda suka yi sau biyu, da yaran da ba su kai ba, da kuma ma na boge waɗanda ba su cika ƙa’idojinmu ba.”

A watan Fabarairu na 2023 ne INEC za ta gudanar da babban zaɓe a Najeriya, inda ‘yan ƙasa za su zaɓi sabon shugaban ƙasa da gwamnonin jiha da ‘yan majalisar jiha da na tarayya.

Labarai Makamanta