Hukumar EFCC Ta Saki Okorochas

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati, EFCC, ta sako tsohon gwamnan jihar Imo, kuma Sanata a yanzu Rochas Okorocha bayan ya yi kwanaki biyu a hannunta yana amsa tambayoyi.

Hadimin Okorocha, wanda ya yi magana da Daily Trust a wayar tarho ya ce an sako tsohon gwamnan misalin karfe 5.45 na yamma kuma a halin yanzu yana gidansa da ke Maitama a Abuja.

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun hukumar na yaki da rashawa, Wilson Uwujaren ya ce a bashi lokaci kafin ya yi tsokaci kan lamarin.

A ranar Talata ne jami’an EFCC suka kama dan majalisar a ofishinsa da ke Unity House Garki Abuja misalin karfe 4 na yamma. Ana zargin Okorocha, wanda ya yi mulki matsayin gwamna a jihar Imo daga shekarar 2011 zuwa 2019 da laifin almundahana da almubazaranci da kudi amma ya musanta hakan.

Labarai Makamanta