Hauhawar Farashin Mai: Buhari Zai Gana Da Gwamnoni

Babban Ministan Kwadago a tarayyar Najeriya Mista Chris Ngige ya ce shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai gana da gwamnonin jihohi inda za su tattauna a kan hauhawar farashin fetur dake tunkarar ƙasar.

Sanata Chris Ngige ya na cewa za ayi wannan zama ne a ranarAlhamis, 25 ga watan Fubrairu, 2021. Chris Ngige ya yi wannan bayani ne a ranar Lahadi, bayan ya jagoranci gwamnatin tarayya yi zaman karshe da kungiyoyin kwadago a fadar Shugaban ƙasa ta Aso Rock.

Ministan ya ce sun duba aikin da kwamitin da aka kafa domin duba farashin man fetur ya yi, kuma ma’aikatarsa ta gabatar da bukatu zuwa ga hukumar NNPC ta ƙasa.

Gwamnatin Tarayya na shirin yin ƙarin kuɗin dakon mai inji shi. “Bangaren kwadago sun lura da matakin gwamnati, kuma kamar yadda na fada, ana cigaba da aiki a kan batun.

Gwamnoni za su zauna a ranar Alhamis.” An yi wannan magana a taron majalisar tattalin arziki, saboda haka kowa ya san halin da ake ciki.

Mun samu kanmu a cikin matsi, babu kudin biyan tallafi. “NNPC sun yi bayani; su na shigo da kaya ne. Idan gwamnati ta zare hannunta, farashi ya danganta ne da yadda kaya su ka zo.”

Sanata Ngige ya ce amma akwai yiwuwar NNPC su samu rangwame wajen shigo da man fetur.

“Kuma su na amfani da kudin kasar waje da aka saida masu ne da rahusa. Ba a kasuwa su ke sayen dala ba.
Saboda haka za a duba duk wadannan idan an zauna”.

Anashi ɓangaren Ministan harkokin mai na Najeriya ya ce ana ta aikin hako mai a Arewa.

Timipre Sylva ya bayyana kokarin da ake yi na samar da mai da ya yi magana kwanaki. Sylva ya koka da cewa annobar COVID-19 ta haifar da koma baya wajen harkar mai da gas a Duniya.

Minista tarayyar ya kuma yi magana game da satar danyen mai da fasa bututu da ake yi, ya ce an samu raguwar wadannan laifuffuka a gwamnatin Muhammadu Buhari.

Labarai Makamanta