Hatsarin Mota Ya Lakume Rayuka A Jihar Bauchi

Rahotanni daga Jihar Bauchi na bayyana cewar Hukumar Kiyayye Hadura Ta Kasa, FRSC, ta ce mutane hudu sun rasu yayin da wasu hudu sun jikkata sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a kauyen Wailo, karamar hukumar Darazo a jihar Bauchi.

Yusuf Abdullahi, Kwamandan hukumar na jihar Bauchi, ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, a ranar Juma’a.

Abdullahi ya ce gudu fiye da kima da yin saɓi zarce ba bisa ka’ida bane ya yi sanadin hatsarin da ya faru misalin karfe 2.45 na yamma wanda ya ci rayukan jama’a da dama.

A cewarsa dukkan mutanen da hatsarin ya shafa maza ne kuma manya. “An kai gawarwakin mutanen hudu da suka mutu a hatsarin zuwa babban asibitin Darazo,” in ji shi.

Ya kuma ce wadanda suka jikkata suna nan a asibitin na Darazo ana musu magani sakamakon cetonsu da jami’an na FRSC suka yi. “Hatsarin ya faru ne tsakanin mota Volkswagen Saloon Golf mai lamba MUB739QW da motar haya kirar Toyota Matrix eagon mai lamba BEN256TA mallakar kungiyar direbobi ta kasa NURTW.

“Jami’an mu, Zebra 45, sun yi bajinta domin sun isa wurin da hatsarin ya faru cikin gaggawa. “Muna da motoccin bada taimakon gaggawa ta kai mutane asibiti a wurare daban-daban domin irin hakan.

“An ajiye su domin su bada taimako da ceto idan anyi hatsari. Sun isa wurin sun kai su asibiti, wadanda suka tsira suna samun sauki a asibiti,” in ji shi. Shugaban na FRSC ya gargadi mutane su rika kiyayye dokokin tuki musamma yawan gudu domin gudun ne ke janyo kimanin kashi 90 cikin 100 na hatsari a kasar.

Labarai Makamanta