Hatsarin Jirgin Sama Ya Kusan Rutsawa Da Sarkin Kano

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Fasinjoji da dama ciki har da Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero sun tsallake rijiya da baya a yayin da jirgin Max Air da ya tashi daga Kano zai tafi Abuja ya samu matsalar inji mintuna 10 bayan tashi daga filin jirgin Kano.

Jirgin na Max Air mai lamba VM1645 wanda ya kamata ya tashi karfe 1.30 na rana amma aka yi jinkiri mintuna 30. Daga baya jirgin ya tashi misalin karfe 2 na rana da fasinjoji cike maƙil.

An gano cewa jirgin ya fara jijjiga a iska kimanin mintuna 10 bayan tashinsa hakan yasa ya yi saukar gaggawa.

Wasu majiyoyi sun ce matsalar inji ne ya janyo lamarin wasu kuma suka ce tsuntsu ne ya yi karo da jirgin.

Da ya ke bada labarin yadda abin ya faru, Dr Sama’ila Suleiman, ɗaya daga cikin fasinjojin da ke jirgin ya ce da ƙyar suka sha yana mai danganta lamarin da sakaci a ɓangaren kamfanin jiragen.

Mr Suleiman ya ce ya ji wani irin sauti na daban a lokacin da jirgin ke tashi amma saidai bai ce komai ba. Ya kara da cewa irin wannan firgicin da suka fuskanta ya saka fasinjoji da yawa cikinsu fasa tafiyar suka koma gidajensu.

Kamfanin Max-Air bai ce komai ba game da lamarin har zuwa lokacin da aka rubuta wannan rahoton.

Labarai Makamanta