Harkar Tsaro Na Habaka A Najeriya – Shugaban ‘Yan Sanda

Rahoton dake shigo mana daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya Usaman Alƙali ya ce ana samun wanzar da tsaro bakin gwargwado, a Najeriya duk da irin kalubalen da ake fuskanta jefi-jefi.

Alkali Baba ya ce a ƙarƙashin sa “zaratan ‘yan sanda na bakin ƙoƙarin su na tabbatar da wanzuwa da ɗorewar zaman lafiya da zaman tare a faɗin ƙasar nan ”

Alƙali ya yi wannan bayani ne a ranar Alhamis, lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, yayin taron sa da ‘yan jarida.

Sai dai kuma wannan iƙirari da Sufeto Janar Alƙali ya yi, ya zo ne daidai lokacin da ake ta samun ƙaruwar kashe-kashe da tashe-tashen hankula a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Sau da yawa kuma ana ƙorafi cewa ko an kira ‘yan sanda domin kai agaji a inda aka kai hari, ba su zuwa sai bayan awa ɗaya da tafiyar mahara, bayan sun yi kisa, sun kuma kwashi waɗanda za su yi garkuwa da su.

Sama da mutum 200 ‘yan bindiga su ka bindige a cikin makonnin da su ka shige.

Sai da kuma IGP Alƙali ya ce rundunar sa na nan na sake nazarin tsarin samar da tsaro a cikin al’umma, domin magance abin da ya kira, “rikice-rikicen da ake samu a cikin jama’a, cikin sassan ƙasar nan.”

“Shirin samar da tsaro na haɗin-guiwa tsakanin ‘yan sanda, sojoji da sauran ɓangarorin jami’an tsaro, ya na ƙarfafa tsaro sosai da sosai ”

Ya ce ana nan ana ta ƙara zaratan ‘yan sanda a wuraren da ake da barazanar matsalar tsaro da yawa.

Labarai Makamanta