Harkar Fim Har Yanzu Ina Jan Zarena Bai Tsinke Ba – Abba Al-Mustapha


Fitaccen Jarumi a Masana’antar shirya fina-finai ta Kannywwod Abba Almustapha yace har yanzu ba a daina yayin sa ba, a cikin Masarautar kannywwod, duk da ba Koda yaushe ake ganin sa a cikin harkar fim din ba.

Jarumin ya bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da Jaridar Dimukaradiyya dangane da masu cewar an daina yayin sa a harkar fim.

Sai yace “Gaskiya ba daina yayina aka yi ba domin mun kafa tarihi a Masana’antar da baza a taba manta damu ba”

Inda ya Kara da cewar “Kowa ya san irin rawar da muka taka a baya, Kuma har yanzu idan na samu lokaci na fito a fim zaka ga yadda Jama’a suke yabawa don haka mu sai godiya ga Allah, domin mun bar tarihin da a harkar fim da ba za a daina yayin mu ba.”

Dangane da rashin ganin sa kuwa a cikin shirin fim, cewa ya yi “To ka San ita harkar rayuwa Kullum ci gaba a ke nema, don haka shekaru uku zuwa hudu da suka wuce na koma karatu a B U K in da na kammala Digiri sannan Kuma na ci gaba har ma a yanzu na Kai matakin karshe Ina daf da kammalawa, Amma dai duk da haka in na samu lokaci na Kan Dan fitowa a fim kamar yadda masu kallo su ke gani.”

Daga karshe ya yi wa masoyan sa dasu ke yi bibiyarsa tare da kara masa kwarin gwiwa masa fatan alheri.

Labarai Makamanta