Al’ummar garin Mutunji dake jihar Zamfara suna cikin halin zulumi da tashin hankali, bayan asarar rayuka mafi muni da garin bai taɓa ganin irin sa ba.
Rahotanni daga garin sun ce a ƙalla mutum 64 ƴan garin ne suka rasa rayukansu bayan da wani jirgin soja ya jefa bam a wani waje da ƴan bindiga suka yi mafaka.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar wa BBC cewa dukkan waɗanda suka mutun maza ne, mafi yawan su ƙananan yara, sai kuma matasa da tsofaffi.
“An yi asarar rayukan da ba a taɓa samun yawan hakan ba a rana guda a garin namu kuma baya ga wadanda suka rasa rayukansu da dama sun jikkata,” ya ce.
Ganau din wanda shi ma ya rasa ƴan uwansa da dama, ya ce an kai waɗanda suka jikkatan asibitin garin Dan Sadau da na Gusau ana duba su.
“Mutum 17 suna asibitin Dan Sadau su kuma 12 da suka fi jin munanan raunuka suna asibitin Gusau duk ana kula da su.
You must log in to post a comment.