Harin Jirgin Abuja: ‘Yan Bindiga Sun Sako Wasu Daga Cikin Fasinjoji

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ‘yan bindigar da suka kai hari tare da sace fasinjoji a jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Abuja sun sako wasu daga cikinsu ranar Asabar.

Mutum 11 ‘yan fashin suka sako saɓanin alƙawarin da suka yi tun farko cewa za su sako dukkan matan da suke tsare da su, kamar yadda mawallafin jaridar Desert Herald Malam Tukur Mamu ya ruwaito.

Tukur wanda shi ne mai shiga tsakanin ‘yan bindigar da kuma gwamnatin tarayya, ya ce mata shida ne da kuma maza biyar aka sako a yanzu bayan shafe tsawon lokaci ana tattaunawa.

Ɗaya daga cikin ‘yan uwan waɗanda aka sako ya tabbatar wa BBC Hausa da sakin ɗan uwan nasu.

Labarai Makamanta