Harin Jirgin Abuja: Iyalan Fasinjoji Sun Shiga Rudani

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Iyalan fasinjojin jirgin kasan da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su bayan harin da suka kai musu akan hanyar Abuja zuwa Kaduna, sun roki shugaban ƙasa Buhari da ya ceci iyalai, ‘yan uwa da abokan nasu, ta hanyar gaggauta amsa bukatar maharan.

Iyalan fasinjojin sun bayyana haka ne, yayin zanga-zangar lumanar da suka yi da safiyar Larabar nan, a cigaba da kokarin jan hankalin gwamnatin tarayya domin ceto ‘yan uwan nasu.

Masu zanga-zangar sun bayyana damuwa kan barazanar da ‘yan ta’addan suka yi na kashe baki dayan mutanen da suka yi garkuwa da su nan da kwanaki bakwai, idan har gwamnatin Buhari ba ta sakar musu ‘yan uwansu. yara 8 da ake tsare da su a jihar Adamawa ba.

Akalla fasinjojin jirgin kasan da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna 61 ne suka shafe kusan watanni 2 a hannun ‘yan bindigar da suka kai musu farmaki a cikin watan Maris, inda suka dasa bam a kan titin jirgin kasan, daga bisani kuma suka bude wuta.

Labarai Makamanta